Ɗan uwan Murtala Sule Garo ya rasu

0
44

Allah ya yiwa Alhaji Abubakar Sule Garo, wanda aka fi sani da Babangida rasuwa.  Marigayin ya kasance babban ɗan uwa ga ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2023 cikin jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Garo.

Babangida, ya rasu a ranar Lahadi, wanda tuni aka yi jana’izar sa a Kofar Kudu dake fadar sarkin Kano, kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Jana’izar ta samu halartar fitattun mutane da suka ƙunshi tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo, kakakin majalisar dokokin Kano, Malaman Islama, yan siyasa da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here