Ɗan majalisar dokokin Kano ya fice daga NNPP zuwa APC

0
72

Dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya fice daga NNPP zuwa APC.

Masu ya sanar da ficewar tasa cikin wata wasikar daya aikewa shugabancin majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin Hon. Ismail Falgore, wadda aka karanta yayin zaman majalisa na yau Litinin.

Ɗan majalisar yace rikicin dake damun NNPP shine babban dalilin sa na yanke shawarar canja sheƙa daga cikin ta.

Yayi jawabin cewa jam’iyyar NNPP na fama da matsalolin shugabanci tun daga jiha har matakin ƙasa, inda ya kafa hujja da cewa ko a Kano jam’iyyar shugabanci biyu ne da ita, na bangaren Hashimu Dungurawa da kuma ɓangaren Sanata Mas’ud Doguwa, sai ƙasa inda ake rikicin shugabanci tsakanin Dr. Ahmed Ajuji da Dr. Agbo Major.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here