Ƙungiyar ASUU ta zabi sabon shugaban ta na ƙasa

0
23

Farfesa Chris Piwuna ya zama sabon shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU).

Piwuna, kwararren likita ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) kuma Shugaban sashin kula da harkokin ɗalibai a Jami’ar Jos da ke Jahar Plateau, wanda ya karɓi wannan mukami daga hannun tsohon shugaban kungiyar ASUU  Farfesa Victor Osodeke, kwararre a fannin kimiyyar ƙasa daga Jami’ar Noma ta Michael Okpara da ke Umudike, a Jihar Abia.

 Piwuna ya lashe zaɓen ASUU bayan fafatawa da Farfesa Adamu Babayo na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), Bauchi wajen neman wannan mukamin.

Zaɓen ya gudana ne a lokacin taron wakilan kungiyar na faɗin Najeriya karo na 23 da aka gudanar a ranar Lahadi a Birnin Benin, na Jihar Edo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here