Farfesa Chris Piwuna ya zama sabon shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU).
Piwuna, kwararren likita ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) kuma Shugaban sashin kula da harkokin ɗalibai a Jami’ar Jos da ke Jahar Plateau, wanda ya karɓi wannan mukami daga hannun tsohon shugaban kungiyar ASUU Farfesa Victor Osodeke, kwararre a fannin kimiyyar ƙasa daga Jami’ar Noma ta Michael Okpara da ke Umudike, a Jihar Abia.
Piwuna ya lashe zaɓen ASUU bayan fafatawa da Farfesa Adamu Babayo na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), Bauchi wajen neman wannan mukamin.
Zaɓen ya gudana ne a lokacin taron wakilan kungiyar na faɗin Najeriya karo na 23 da aka gudanar a ranar Lahadi a Birnin Benin, na Jihar Edo.