Nijar ta haramta fitar da dabbobi zuwa ketare

0
71

Ma’aikatar bunkasa kasuwanci ta Jamhuriyar Nijar ta sanar da haramta fitar da dabbobi daga kasar zuwa kasashen ketare domin kauce wa tashin farashin dabbobi kafin bikin Babbar Sallar. 

Ministan kasuwanci, Abdoulaye Seydou, ya ce matakin hana fitar da shanu, tumaki, awaki da rakuma an dauke shi ne domin tabbatar da wadatar dabbobi a kasuwannin cikin gida kafin lokacin Sallar Layya, yana mai gargadin hukunci kan duk wanda ya karya wannan doka.

A Nijar, kasa da fiye da kashi 90 cikin 100 na al’ummarta Musulmai ne, ana yanka dubban raguna a yayin Sallar Layya don haka a cewar gwamnatin mulkin sojin kasar akwai bukatar wadatar da gida kafin fitarwa ketare.

DW Hausa, ta rawaito cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda a Nijar da yankin Sahel na yawan sace dabbobi, wanda hakan ke sa makiyaya su tsere daga kauyukansu kuma farashi ya karu. Baya ga haka, satar dabbobi na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kudin shiga ga kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Boko Haram, inda mayakansu ke sayar da wasu dabbobi a kasuwannin cikin gida yayin da suke fitar da wasu domin tallafa wa ayyukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here