Hukumar Kashe Gobara ta birnin tarayya ta fitar da sanarwar neman afuwa bayan da ɗaya daga cikin motocin ta tayi taho mu gama da wata mota, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane uku da raunata mutum ɗaya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Kwamandan hukumar a babban birnin tarayya Abuja, Momodu Ganiyu, ya bayyana cewa hukumar na cikin bakin ciki da nadama game da wannan mummunan lamari.
Lamarin ya faru da yammacin ranar Juma’a a kusa da mahaɗar titin ECOWAS da ke Wuse 2, yayin da ake aikin kashe gobara a wani wuri mai suna Avenue Plaza, Banex.
Sanarwar tace motar na tafiya da sauri tare da karar karar jiniya kafin ta ci karo da wata mota kirar Toyota Camry da ke fitowa daga wata hanya.