Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar PDP a zaɓen shekarar 2023 Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC kan tsare tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Muhammad Gudaji Kazaure.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya kwatanta kama Gudaji Kazaure da kuma tsare shi a matsayin saɓa wa doka.
Atiku yace EFCC ta sake aikata abin da ta saba yi na take doka, ta hanyar kamawa da kuma tsare ƴan ƙasa da ba su aikata laifin komai ba.
Ya yi misali da labarin fitattcen ɗan gwagwarmayar nan Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman wanda EFCC ta kama amma ta sake shi bayan matsin lamba daga wajen ƴan ƙasa.
Ya ce ko da akwai abin da mutum ya aikata to ya kamata a bi hanyar shari’a wajen gurfanar da shi.