An kuɓutar da wata yarinya da aka siyar a Abuja

0
50

Hukumar yaƙi da fataucin mutane ta ƙasa NAPTIP ta ce ta ceto wata yarinya ƴar shekara biyu da aka yi safararta zuwa jihar Abia daga birnin tarayya Abuja.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma’a, ta ce jami’an tsaron farin kaya (DSS) ne suka kama wanda ya yi safarar, inda ake zargin ya sayar da da ita kan naira 100,000.

NAPTIP tace ana zargin wanda ya yi safarar yarinyar mai suna Chiamaka Favor, ya yi aiki da wasu ƙungiyoyin safarar mutane uku a Abuja, sannan ya sayar da ita ga wani.

Hukumar ta kuma yi kira ga iyayen yarinyar ko ƴan uwanta da su hanzarta su tuntuɓe ta domin karɓar ƴarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here