Shugaban ƙasa Tinubu ya kare matakan da yake ɗauka na sauye-sauyen tattalin arziki inda ya ce daukar matakin wata hanya ce ta samun cigaban ƙasa.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Juma’a a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja, lokacin da ya karɓi bakuncin jakada na musamman daga ƙasar Qatar, Dr. Mohammed bin Abdulaziz Al-Khulaifi.
Tinubu ya ce tsare-tsare da ake ɗauka na inganta harkar haraji a Najeriya, ya sa mutane daga ƙasashen waje na samun saukin zuba-jari da yin kuma kasuwanci.
A cewar shugaban, yana yin kokari wajen gyara tsarin harajin Najeriya, da bijiro da sabbin hanyoyin cigaban fannin saboda irin ƙalubalen da aka fuskanta a baya, sannan yace duk tsaurin da ake samu saboda wannan tsari zai zama mai amfani a nan gaba.
Tinubu, yace gwamnatin sa zata zage damtse wajen yaƙar talauci a tsakanin yan Najeriya, da inganta ayyukan jinƙai.
Ita dai gwamnatin Tinubu, ta da manufofi masu ciwo musamman ga talaka, saboda tsadar rayuwar da aka afka bayan da ya ayyana cire tallafin man fetur, da mayar da canjin kudaden ketare zuwa tsarin bai ɗaya.