Jagororin arewa na gudanar da taron nemowa yankin mafita

0
39

Gwamnonin da sarakunan na gudanar da wani taro a jihar Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin da suka dabaibaye yankin musamman rashin tsaro da sauran su.

Taron wanda ke gudana a gidan gwamnatin jihar Kaduna, zai kuma tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke addabi arewa.

Gwamnonin jihohin Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da kuma Zamfara na cikin waÉ—anda ke halartar taron.

A É“angaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here