Indiya da Pakistan sun tsagaita wutar yaƙin da suka fara

0
111

Kasashen Indiya da Pakistan, sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da suka fara, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar.

Shugaban na Amurka yace yarjejeniyar tsagaita wutar ta nan take ce, wadda ta ƙunshi cikakkiyar tsayawar yaƙin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane, bayan harbe harben makamai masu linzami a tsakanin kasashen biyu.

Tuni dai hukumomin kasar Pakistan suka sanar da cewa an dawo da hada hadar sufurin jiragen sama kamar yadda aka saba, bayan dakatarwar da aka yi a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here