Gwamnatin Borno ta hana siyar da fetur a wasu garuruwan jihar

0
24

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, haramta sayar da man fetur a karamar hukumar Bama da garin Banki.

Gwamnan ya ce umarnin haramcin ya zo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka domin shawo kan matsalolin tsaro da Borno ke fuskanta.

Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaÉ—a labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani É“angare ne na matakan da gwamnati ke É—auka don daÆ™ile ayyukan Æ´an ta’adda.

Gwamnan ya yi gargaÉ—in cewa duk wanda aka samu yana saÉ“a umarnin hana sayar da man zai fuskanci hukunci mai tsanani, saboda babu wanda doka za ta kyale, sannan babu wanda za’a É—auke kai akan sa in ya aikata hakan.

Gwamnan ya bai wa hukumomin tsaro damar kama duk wani gidan mai ko kuma mutum da ya take wannan umarnin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here