Rundunar ƴan sandan Kano ta kama muggan kwayoyi da ƴan fashi

0
27

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama masu laifi 78, tare da kama muggan makamai da miyagun ƙwayoyi, haɗi da kama wasu kayan da aka sato.

Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da hakan a yau juma’a, yayin da yake jawabi ga manema labarai, a shalkwatar yan sandan dake Bompai, inda yace an samu nasarar yin wannan kame a samamen da jami’an su suka kai a yan kwanakin nan.

Yace a yayin samamen, an kama babban dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022.

Daga cikin sauran wadanda aka kama akwai wani da ake zargin dan fashi da makami ne da bindigogi biyu da harsasai.

Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya ƙara da cewa jami’an rundunar yan sandan sun kama masu laifin bayan samun bayanan sirri da samun tallafin a’lummar Kano.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigogi, miyagun kwayoyi, motoci, babura mai kafa uku, babura, muggan makamai, kudin jabu, dabbobi, da kayan lantarki.

Kwamishina Bakori ya jaddada alakar da ke tsakanin safarar miyagun kwayoyi da aikata laifuka masu hadari, yana mai cewa kama mutanen da kwace kayayyakin sun nuna irin nasarar da ake samu wajen rage irin wadannan laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here