Kotu ta kori ƙarar da kamfanin shirya fina-finai na Amart ya shigar akan masu sana’ar tura fina-finai

0
19

Kamfanin Amart Enterprises ya yi rashin nasara a karar da suka shigar da Hukumar tace fina-finai gaban kotu kan neman abasu damar cigaba da kama masu sana’ar tura fina-finai wato downloading.

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a unguwar kotu road cikin birnin Kano ta Kori karar da kamfanin shirya fina-finan Kannywood, na Amart Enterprises ya shigar da Hukumar tace fina-finai bisa neman kotun da ta hana Hukumar tace fina-finai dakatar dasu kan cigaba da kama masu sana’ar tura fina-finai wato downloading a Jahar Kano da sunan kamfanin sun mallaki lasisin hana wani yin amfani da finafinan da suka fitar wato copyright.

A zaman da kotun ta yi a lokacin yanke hukunci Mai shari’a Simon A. Amobeda ya ce kotun bata da hurumin sauraran karar Hajiya Aisha Amart a saboda haka ya Kori karar.

Tsawon lokuta tun a baya kamfanin Amart Enterprises ya shiga takun saka da Hukumar tace fina-finai biyo bayan karar da masu sana’ar tura fina-finai ta downloading na Jahar Kano suka rubutawa Hukumar kan irin gallazawar da suke zargin Hajiya Aisha Amart nayi musu da sunan copyright inda ake kamasu tare da dora musu tara mai tsanani da sunan hukunci.

Sai dai bayan karbar korafe korafen matasan Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya nemi kamfanin domin kawo gyara inda dukkannin bangarorin biyu suka yadda da tsarin da a kazo da shi domin tsaftace kurakuren da ake samu wanda daga baya Aisha Amart ta karya tsarin inda hakan yasa Hukumar tasa kafar wando daya da ita dalilin da yasa ta garzaya gaban kotu.

Bayan yanke wannan hukunci Abba El-mustapha ya godewa Allah tare da Kara tabbatar da aniyarsa ta tabbatar da yin adalci ga kowa da kowa ba tare da nuna banbanci ba ko wata alaka ta aiki a masana’antar kannywood.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here