Hukumar shirya jarrabawar neman gurbi a makarantun gaba da sakandire, (JAMB) ta riƙe sakamakon jarrabawar wannan shekara na ɗalibai kusan dubu 40.
Hukumar JAMB ce ta sanar da hakan a yau juma’a, bayan sakin sakamakon jarrabawar ta shekarar 2025.
Hukumar shirya jarrabawar tace a yanzu haka tana riƙe da sakamakon dalibai 39,834, da aka tabbatar sun aikata wasu abubuwan da suka saɓawa ka’ida yayin rubuta jarrabawar.
JAMB ta kara da cewa an kama dalibai 80 da zargin aikata wasu laifuka yayin jarrabawar, wanda a halin yanzu suke fuskantar tuhuma, kamar yadda shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, ya sanar a yau Juma’a.
Akalla dalibai miliyan 1 da dubu ɗari 9, ne suka zana jarabawar JAMB a wannan shekara ta 2025.