Gwamnatin Kano zata kashe biliyan 3 wajen biyawa dalibai kuɗin NECO

0
28

Gwamnatin Kano ta amince da kashe sama da naira miliyan dubu 3 domin biyawa daliban jihar kuɗin Jarabawar kammala sakandire ta ƙasa wato NECO.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Alhaji Ali Haruna Makoda ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa a ranar Juma’a.

Kwamishinan yace dalibai 141,715 ne suka rubuta Jarabawar neman cancantar samun damar rubuta NECO kyauta daga gwamnati ko kuma dalibi ya biyawa kansa in bai yi nasara ba, wato jarrabawar Qualifying, inda ya sanar y cewa kaso 75 cikin 100 na daliban sun samu nasara.

Daliban da zasu amfana da kuɗin tallafin sun hada da wadanda zasu rubuta jarabawar NECO da NAPTIB da NBAIS.

Ali Makoda yace biyawa daliban jihar Kano jarabawar ta NECO,yana daga cikin burin gwamnati na ingata ilimi a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here