Matsalar ƙarancin wutar lantarki a asibitocin Najeriya na jefa marasa lafiya cikin halin ƙunci, wanda hakan ke haddasa asarar rayukan masu jinya a wasu lokutan.
Rahoton jaridar Aminiya, ya bayyana cewar rashin wutar ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatar haihuwa, wata kuma ta mutu sakamakon dauke wuta a yayin da ake tsaka da yi mata tiyata, a Asibitin Jummai Babangida Aliyu, da ke jihar Neja.
Jaridar tace an shafe sama da kwana uku a jere babu wutar lantarki a asibitin gwamnatin, a yayin da rashin wuta da yanayi na tsananin zafi ya tilasta wa ’yan uwan majinyata amfani da fankoki masu amfani da caji domin samun iska a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Jihar kano.
Sai dai a cikin wannan hali, Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar da shirin sake kara kudin wutar, bisa hujjar cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin lantarki ba.