Shugaban ƙasa Tinubu ya kafa wani kwamiti na musamman da zai yi duba akan yadda za’a cire dukkan wasu shingen da ake da su a kan iyakokin ƙasar nan don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye.
Wakilin Najeriya a kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, Amabasada Musa Nuhu, ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin a ranar Laraba.
Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanyar Iyakar Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.
Ambasada Nuhu ya ce hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al’umma.
Shugaban hukumar ECOWAS Omar Alieu Touray, ya yi, Allah wadai kan yadda jamai’an tsaron da ke kula da shingayen da ke hanyar ke ƙarɓar kuɗi a hanun al’ummar ƙasashe daban-daban da ke shige da fice a ƙasar nan, wanda ya ce hakan, ya saɓa da shirin ECOWAS na haɗe yankin wuri ɗaya.