Shugaban ƙasa Tinubu ya kai ziyarar aiki jihar Anambra

0
19

Shugaban ƙasa Tinubu, ya kai ziyarar aiki zuwa Anambra, a yau Alhamis tare da buɗe wasu ayyukan da gwamnatin jihar tayi karkashin jagorancin Gwamna Chukwuma Soludo.

Cikin ayyukan da Tinubu ya buɗe akwai sabon gidan Gwamnatin jihar da aka gina, sai sabunta ginin majalisar dokokin jihar, da wasu gidajen alfarma da aka gina da sauran manyan ayyuka.

Tinubu, ya sauka a jihar ta Anambra da misalin karfe 12:14, na rana a filin tashi da saukar jiragen sama na Chinua Achebe, tare da rakiyar mai bawa shugaban ƙasa shawara a fannin tsaro Nuhu Ribadu, Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, Gwamnan Imo Hope Uzodinma, Gwamnan Enugu Peter Mbah, da ministan ayyuka David Umahi da sauran su.

A yayin buɗe sabon gidan Gwamnatin jihar ta Anambra, Tinubu, ya bayyana Gwamna Chukwuma Soludo, a matsayin mai kokarin kawo cigaba Anambra ta fannin ayyukan raya ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here