Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi zargin cewa sojoji, ƴan sanda da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’ar ƙasar nan.
Zulum ya bayyan hakan a ranar Talata lokacin da yake haramta sayar da giya a Borno.
Gwamnan ya kuma ƙaddamar da wani kwamitin da aka samar don ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana na maɓoyar masu aikata miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan ɗabi’u.
Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka irin su tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da yace shine ke ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar.
Yace wasu daga cikinsu akwai jami’an soji da aka kora da masu ci a yanzu har da fararen hula.