Ba mune muka haramta yin hirar siyasa kai tsaye ba—Gwamnatin Kano

0
36
Abba Gida Gida
Abba Gida Gida

Gwamnatin Kano ta musanta cewa itace ta ɗauki matakin haramta yin hirar siyasa kai tsaye a kafafen yaɗa labarai na jihar, inda ta kafa hujjar cewa mamallaka kafafen yada labarai ne suka yanke wannan hukunci da kansu, don takaita cin zarafin juna, da tattaunawar siyasa mai zafi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan cikin wata zantawar da yayi da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa.

Kwamishinan yace masu kafafen yaɗa labaran ne suka ga dacewar hakan domin tabbatar da zaman lafiya da girmama juna a Kano baki daya.

Idan za’a iya tunawa dai, a yau Alhamis ne aka wayi gari da samun wata sanarwa daga ma’aikatar yaɗa labarai da al’amuran cikin gida ta Kano, mai nuni da cewa dag yanzu an hana yin tattaunawar siyasa kai tsaye a kafafen watsa labarai na jihar Kano, sannan an hana masu gabatar da shirye-shiryen siyasa yin tambayoyin da zasu sanya a bayar da amsa mai zafi a hirarrakkin siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here