Wata kotun majistre ta aike da wasu maza su 10 zuwa gidan gyaran hali sakamakon yin fyade ga wata mai buƙata ta musamman ƴar shekara 14, a garin Likoro dake ƙaramar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, a daidai lokacin da ake cigaba da neman mutum na 11 da aka aikata fyaden tare da shi.
Rahotan da aka gabatarwa kotun ya bayyana cewa mutane 11, sun riƙa yiwa ƙaramar yarinyar fyade a mabanbantan lokuta sannan a waje daban-daban, wanda hakan ya kai ta ga ɗaukar ciki, tare da haifar yaro mai kimanin watanni 4 a halin yanzu.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Sifeta Yakubu I. Lemu, ya sanar da kotu cewa laifin da ake tuhumar mutanen da aikatawa ya saɓawa sashi na 257, na kundin Penal Code, na jihar Kaduna.
Ɗan sandan ya ƙara da cewa a ranar 27 ga watan Oktoba na shekarar 2024, wani mai suna Usmanu Yusuf, ya kaiwa jami’an tsaro rahotan cewa an yiwa ƙanwar sa mai suna Fatima Maikanti, ciki, tsawon watanni 6, wanda bincike ya tabbatar da cewa wasu maza ne su 11 suka riƙa yin lalata da ita tsawon lokaci har takai ga samun juna biyu.
Daga haka ne mai Shari’a Abubakar Lamido, ya bayar da umurnin tsare waɗanda ake zargin, tare da cewa suna jiran karɓar shawarwari daga ma’aikatar Shari’a ta Kaduna kafin yanke hukunci, sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Mayu.