Rikici ya haifar da tangarɗa a sifurin jiragen saman Indiya da Pakistan

0
32

Hare-haren da Indiya ta kaiwa Pakistan sun janyo dakatar da tashin kusan jiragen sama 550 a tsakanin ƙasashen biyu.

Bayan harin jiragen sama da aka kai, an dakatar da tashin jirage 135 a Pakistan, yayin da a Indiya jirage 417 aka dakatar, kamar yadda bayanan na’urar da ke bibiyar jirage kai tsaye na Flightradar24 suka nuna.

A yau Laraba, an ga fasinjoji cike a filin jirgin Sama na Jinnah da ke Karachi, suna jiran jiragen.

Pakistan dai ta sanar da cewa indiya ta kai mata hare hare wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 8, da jikkata 35, a daidai lokacin da aka harbo jiragen yakin Indiya, guda 5, sakamakon rikicin dake tsakanin su akan wani yanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here