Harin India ya kashe mutane da dama a Pakistan

0
69

Indiya ta kashe mutane 7, tare da jikkata 35, a harin makamai masu linzami da ta kaiwa Pakistan a cikin dare.

Sojojin Saman Pakistan sun harbo jiragen yaƙin India biyar bayan India ta kutsa cikin ƙasarsu inda ta kashe fararen-hula takwas da jikkata mutum 35, a cewar Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif. 

Sun ɗauki wannan mataki ne bayan India ta harba makamai masu linzami a cikin Pakistan lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas tare da jikkata aƙalla mutum 35 sannan mutum biyu sun ɓata.

Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ce an harbo jiragen yaƙin India biyar kuma an yi garkuwa da sojojin India takwas a matsayin fursunonin yaƙi.

Tun da farko, Ministan Watsa Labaran Pakistan Attaullah Tarar ya shaida wa TRT World cewa an harbo jirgi guda ɗaya a birnin Akhnoor da ke yankin Kashmir wanda ake taƙaddama a kansa, sannan aka harbo wani jirgin a birnin Ambala na ƙasar India, kazalika an harbo jirgi marasa matuƙi a lardin Jammu na ɓangaren Kashmir da ke ƙarƙashin ikon India.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here