Daga kan shugaban ƙasa ya kamata a fara aiwatar da dokar hana shigo da kayayyaki Najeriya—Atiku

0
18

 Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya kalubalanci Shugaban kasa Bola Tinubu, da ya sauya motocinsa da sauran motocin da fadar gwamnatin ke amfani da su, zuwa amfani da kirar gida Najeriya.

Atiku ya kalubalanci Tinubu biyo bayan wata sanarwa da ministan yada labarai Muhammad Idris, ya fitar akan haramta shigo da irin kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya. 

A cewar Atiku ya kamata Tinubu idan har da gaske yake yana son inganta tattalin arziƙin Najeriya, ya kamata ya sauya motocinsa da ƙirar kamfanonin Innoson, Nord da sauransu wanda ake haɗawa a nan gida.

A ranar Litinin, Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta amince da wani sabon tsarin “Nigeria First” da ke baiwa kayan da aka samarwa a gida fifiko a duk wani tsarin siye da siyarwa na gwamnati.

Ministan yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan bayan taron da zartarwa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce za a karfafa wannan doka ta hanyar umarnin shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here