Burtaniya na shirin dena bawa ƴan Najeriya, da wasu ƙasashe Visa

0
30

A wani shirin yin kwaskwarima ga tsarin shige da fice, na Burtaniya, nan ba da jimawa ba ƙasar za ta dakatar da bada shaidar shiga cikin ta ga yan wasu kasashe sakamakon kin dawowa gida da ƴan ƙasashen ke yi lokacin da wa’adin zaman su ya ƙare.

Jaridar Times ta, ruwaito cewa babban Ofishin cikin gida na Burtaniya ya lissafa kasashen da abin ya shafa da suka hada da Pakistan, Najeriya, da Sri Lanka.

Rahoton ya yi nuni da cewa mutanen wadannan kasashe suna wuce lokacin wa’adin Visar su inda daga baya su ke neman mafaka.

Sakamakon haka, Ofishin Cikin Gida na Burtaniya akan shige da fice ya ce masu yin irin haka ka iya fuskantar kin yi musu Visa lokacin neman aiki ko karatu a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here