Babu gaskiya a zargin cewa mayaƙan Boko Haram, sun fi Sojoji makamai—Ministan tsaro

0
25

Ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar, ya musanta zargin da wasu yan majalisar dokokin kasa suka yi na cewa mayaƙan Boko Haram da sauran ƴan ta’adda sun mallaki makaman da suka fi na jami’an tsaro kyau, yana mai cewa zargin ba gaskiya bane kuma hakan zai iya karkatar da hankulan al’umma.

Badaru, ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake jawabi a wajen taron da ministoci ke bayyana ayyukan ma’aikatun su na shekarar 2025 a Abuja.

Ministan ya jaddada cewa babu wasu yan ta’addan da suke ɗauke da makaman da suka fi karfin na jami’an tsaron kasar nan.

Sai dai yace suna nan suna bibiyar hanyoyin da ƴan ta’adda ke bi wajen mallakar jirage mara matuƙi, inda yace ko a yanzu gwamnati ta ci ƙarfin mayaƙan.

Idan za’a iya tunawa wasu mambobin majalisar wakilai daga jihar Borno, sun tabbatar da cewa mayaƙan Boko Haram, na yin amfani da jiragen yaki mara matuƙi wanda ko sojojin Najeriya basu da irin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here