Ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, yace ba shugaban ƙasa Tinubu, ne ya cire tallafin man fetur ba, shi sanarwa kawai yayi, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasa Buhari ne ya cire tallafin.
Kawu, ya sanar da hakan ne lokacin da aka yi wata zantawa da shi a tashar talabijin ta Channels, a daren jiya Talata.
A cewar Kawu, tun kafin saukar Buhari, daga mulki gwamnatin sa ta tsara cire tallafin, wanda shi kuma Tinubu, ya sanar da cirewar lokacin da ya karɓi mulkin ƙasar nan.
A cikin hujjar da Sanatan ya kafa akwai cewa Kasafin kuɗin karshe na gwamnatin Buhari, bai tsara biyan tallafin mai ba.
Tuni dai kalaman nasa ya fara fara haifar da cece kuce, tsakanin yan Najeriya, masu ganin cewa gwamnatin Tinubu ce ta cire tallafin man fetur.