Ƙwazon Tinubu ne yasa ƴan jam’iyyun adawa ke rububin dawowa APC—Gwamnan Nasarawa

0
19

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, yace ƙwazon shugaban ƙasa Tinubu ne yasa ƴan jam’iyyun adawa ke rububin dawowa APC.

Kamar dai yadda ake gani a ɗan lokacin nan, fitattun yan siyasa magoya bayan jam’iyyun adawa daban daban, ne ke rububin dawowa APC a faɗin Najeriya, wanda daga cikin su akwai tsohon gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, da gwamnan jihar mai ci a yanzu da kuma yan majalisar wakilan jihar.

Sauyin shekar yan siyasar dai na haifar da cece kuce, akan zargin shugaban ƙasa Tinubu, da kokarin mayar da Najeriya ƙasar dake yin siyasar jam’iyya ɗaya.

 Amma Gwamna Abdullahi Sule, bayan wata ganawar da yayi da shugaban ƙasa, ya bayyanawa manema labarai cewa zargin da ake yiwa Tinubu bashi da tushe balle Makama, inda yace kokarin Tinubu ne yasa ake komowa APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here