Rashin tsaro ya tilastawa a’lummar Sabon Birni yin hijira

0
74

Rahotanni sun bayyana cewa ayyukan yan fashin daji da sauran ƴan ta’addan da suka addabi jihar Sokoto ya tilastawa kaso mai yawa na a’lummar karamar hukumar Sabon Birni, yin hijira don tsira da rayuwar su.

Daya daga cikin al’ummar dake rayuwa a yankin mai suna Abdulrazaq Dunkawa, ya bayyanawa Daily News 24 Hausa, cewa sun jima suna fama da rashin tsaro, wanda ya ƙunshi garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, kisan gillar mutane da farmakar manoma.

A cewar sa, bangarorin ilimi da noma ne suka fi fuskantar kalubalen rashin tsaron, wanda hakan ya gurgunta noma da harkokin neman ilimi musamman a yankunan karkara, sannan kaso 80 cikin ɗari na mazauna ƙaramar hukumar sun dogara da noma wajen yin rayuwar yau da kullum, amma a yanzu noman ya gagara saboda yadda ake kashe manoma babu kakkautawa.

Abdulrazaq Dunkawa, ya kara da cewa yan ta’addan sun kuma saka haraji ga mutanen da suka zaɓi cigaba da yin rayuwa a ƙauyukan su, tare da yiwa mata fyade da kisan kananun yara, wanda hakan ya sanya dole mutane su miƙa wuya ga bata garin.

A bangare guda, a’lummar Sabon Birni, sun ɗora alhakin ƙaruwar rashin tsaron yankin akan janye dakarun sojin dake bayar da tsaro a yankin.

A’lummar sun roƙi gwamnatin tarayya akan ta taimaka musu da ɗaukin jami’an tsaron da zasu taimaka wajen dawowa da yankin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here