Nnamdi Kanu ya karyata lauyan da ke kare shi ana tsaka da zaman kotu

0
68

An fuskanci hargitsi a babbar kotun tarayya dake Abuja, a yau Talata yayin da shugaban haramtacciyar ƙungiyar, masu rajin kafa kasar Biapra IPOB , Mazi Nnamdi Kanu, ya karyata wani lauya mai suna Charles Ude da ya bayyana kansa a matsayin wanda ke wakiltarsa.

Kanu dai na fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi ta’addanci da cin amanar ƙasa tsakanin sa da gwamnatin tarayya.

A lokacin zaman kotun, alkalin da ke jagorantar shari’ar ya jawo hankalin ɓangarorin da ke cikin shari’ar zuwa wata wasika daga Charles Ude, wanda ya ce shi ne lauya na gaskiya da ke kare Kanu.

Sai dai tawagar lauyoyin da ke kare Kanu sun ce ba su san Ude ba, kuma Kanu da kansa ya tabbatar da hakan, yana mai jaddada cewa Agabi ne kawai lauyansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here