Asusun tallafawa ƙananun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) ya bayyana cewa Najeriya ce ke da mafi yawan yara masu fama da matsanancin ƙarancin abincin masu gina jiki a nahiyar Afirka.
A cewar sanarwar da asusun ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Talata, daga cikin yara 10 da ke fama da wannan matsala biyu ne kawai ke samun magani.
Asusun ya bayyana cewa kimanin yara miliyan biyu ne a Najeriya ke fama da mmatsalar ta tamowa, inda hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan yaran da ba su girma yadda ya kamata kuma ta biyu a duniya, da kashi 32 cikin 100 na yara ‘yan ƙasa da shekara biyar.
Hakazalika, Unicef ya ce kashi 7 cikin 100 na mata masu haihuwa a Najeriya na fama da matsanancin ƙarancin abinci.
Asusun ya nuna damuwa kan yadda ƙarancin abinci ke haddasa kashi 45 cikin 100 na mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekara biyar tare da barazana ga lafiyar jama’a da tattalin arziki.