Ƙungiyar kananan likitoci ta ƙasa reshen birnin tarayya Abuja, sun sanar da shirin su na fara yajin aiki na gargadi tsawon kwanaki 3 wanda za’a fara daga yau Talata.
Ƙungiyar likitocin ta ɗauki wannan mataki don ƙalubalantar matakin da hukumar kula da ma’aikatan birnin ta ɗauka na korar wasu ma’aikatan lafiya su 127
Tashar talabijin ta Channels, ta rawaito cewa likitocin sun yanke shawarar shiga yajin aikin bayan gudanar da wani taron gaggawa a asibitin Asokoro, a ranar Litinin data gabata.
Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr. George Ebong, ya bayyana korar a matsayin maras tushe da kuma “rashin imani”, yana mai buƙatar gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu.
Dr. Ebong ya kuma buƙaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja Nyesom Wike bai ɗauki mataki cikin kwanaki uku ba za su shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani tare da rufe duk asibitocin Abuja.