Gwamna Dikko Umar Raɗɗa, yace bai san an kafa allon cewa Katsina babu ƙorafi ba, a lokacin ziyarar shugaba Tinubu zuwa jihar Katsina.
Raɗɗa, yace akwai kuskure mutane su riƙa yaɗa abinda basu da tabbas akai, yana mai cewa shima a kafafen sada zumunta ya samu labarin kafe allon cewa Katsina babu ƙorafi.
Akan haka ne gwamnan yace kowa zai iya yin kuskure, don haka mutane su riƙa yin tambaya ko neman ƙarin bayani kafin yin magana akan abun da basu tabbatar ba.
Shi dai wannan allo na Katsina babu ƙorafi, an kafa shi a Katsina lokacin da ake gaf da ziyarar Tinubu, da ya buɗe wasu ayyukan gwamnatin jihar da kuma halartar taron daurin auren ƴar Gwamna Raɗɗa.
Babban abin da ya jawo hankalin al’umma akan kafa allon shine, yadda taɓarɓarewar sha’anin tsaro ya mamaye Katsina, duk da haka kuma a ce babu wani korafi ga mahukunta musamman shugaban ƙasa, wanda a hannun sa alhakin kula da tsaron ƙasa yake.