Kananun yara 5 sun mutu a motar da aka ajiye

1
441

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta bayar da umarnin gudanar da bincike akan dalilin da ya sanya aka samu rasuwar wasu kananun yara su 5, a cikin wata motar da take ajiye sakamakon dena yin amfani da ita. Kwamishinan yan sandan Shetima Jauro-Mohammed, ne ya bayar da umarnin gudanar da binciken, bayan samun gawar yaran a yankin Agyaragu, dake karamar hukumar Obi.

:::Wata budurwa ta kashe saurayinta a Nasarawa

Kakakin rundunar yan sandan Nasarawa SP Rahman Nansel, ne ya sanar da hakan a yau litinin lokacin da yake yin jawabi a Lafia.

Nansel, yace an samu gawarwakin yaran a cikin motar data lalace wadda aka ajiye a gidan wani mutum mai suna Abu Agyeme, yana mai cewa kwamishinan yan sandan ya bayar da umarnin gabatar da babban binciken dalilin mutuwar yaran, tare da bayyana jimami da takaicin samun labarin lamarin, inda ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyayen mamatan.

Bayan haka rundunar yan sandan ta nemi iyaye su rika sanya idanu akan ababen hawan da suke ajiyewa a gida sakamakon lalacewa don gujewa faruwar irin wannan abu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here