Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari zuwa wani sansanin soji a jihar Yobe.
Kamar yadda jaridu suka rawaito an kai harin kan sansanin sojojin dake Buni Yadi na ƙaramar hukumar Gujba a tsakar daren Asabar.
Wani daga cikin al’ummar Yobe, ya bayyana cewa mayaÆ™an sunyi barna mai yawa, tare da yiwa sojoji yankan rago.
A baya bayan nan dai hare haren yan Boko Haram, na neman dawowa musamman a jihohin Borno da Yobe, wanda ko a yan kwanakin nan sai da mayaƙan ISWAP suka ɗauki alhakin kisan wasu mutane 26 a Borno.