Sarkin Kano na 16 Muhammad Sanusi II ya gudanar da sabbin naɗe naɗe

0
48

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci tawagar jami’an gwamnatin Kano zuwa fadar Sarkin Kano dake Kofar Kudu, don halartar taron bikin sabbin naɗe naɗe da sarki Muhammad Sunusi II, ya gudanar.

Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, shine ya jagoranci yin sabbin naɗe naɗen a yau juma’a.

Wadanda aka naɗa sun haɗar da;

1. Alhaji Munnir Sanusi Bayero a matsayin Galadiman Kano.

2. Alhaji Kabir Tijjani Hashim a matsayin Wamban Kano.

3. Alhaji Mahmud Ado Bayero a matsayin Turakin Kano 

4. Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a Matsayin Yariman Kano.

5. Alhaji Adam Lamido Sanusi a Matsayin Tafidan Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here