Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa sabon Galadima

0
55

 Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano. 

Sarkin Kano yace an nada Alhaji Sunusi Ado Bayero ne a matsayin Galadiman Kano saboda cancanta da Kwazonsa da irin gudunmawa da yake bayarwa ga cigaban  Masarautar Kano da al’ummar jihar Kano da kasa baki daya.

Yace Sabon Galadiman yana da gogewa a fannoni daban daban inda yayi aiki a matakin Gwamnatin Jiha da yakai matsayin Babban Sakataren wato (Permanent Secretary) a matakin Gwamnatin Tarayya kuwa ya rike mukamin Babban Shugaban Tashoshin jiragen ruwa ta kasa wato (MD Port Authority) . 

Sarkin yace ya zuwa yanzu Sabon Galadiman yana rike da sarauta sama da shekara ar’bain a matakai daban daban, inda yace hakan ce tasa suke alfahari da irin gogewarsa a fannin aikin Gwamnati da Sarauta.

Yayi fatan wannan Matsayi da Allah ya bashi zai kara masa karsashi don kare martabar Masarautar Kano kamar yadda ya saba a shekarun baya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here