Hukumar ICPC ta janye kalaman ta na cewa an karkatar da Naira biliyan 71.2, a kuɗin tallafin bashin karatu na gwamnatin tarayya.
Da farko dai hukumar tayi bayanin cewa an rasa inda aka kai waɗancan kuɗaɗe, tare da gayyato manyan jami’an gwamnatin tarayya don bayyana inda aka kai kuɗin.

Amma a yanzu hukumar tace tayi kuskure a sanarwar da ta fitar.