Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta neman a yiwa dokokin zabe na shekarar 1999 da 2022 kwaskwarima.
INEC ta nemi hakan a lokacin da jami’an ta ke ganawa da kwamitocin majalisun dokokin ƙasa masu kula da hukumar, inda mai taimakawa Farfesa Mahmud Yakubu shugaban INEC, na musamman Mohammed Kuna, yace akwai bukatar lallai a yiwa dokokin zaɓe gyara.
Kuna yace a cikin gyaran da suke nema akwai bukatar bawa hukumar damar naɗa kwamishinonin hukumar zaɓen jihohi sakamakon cewa shugaban ƙasa ne ke da alhakin naɗawa a yanzu.