Gwamnonin yankin arewa maso gabashin kasar nan sun shirya wani babban taro don bibiyar matsalolin da suke ciki da kuma lalubo hanyar magance su.
Taron dai na gudana a yau Alhamis, a birnin Damaturu na jihar Yobe.
Wannan taro yazo a daidai lokacin da hare haren Æ´an ta’adda suka tsananta a yankin, musamman harin yan Boko Haram.
Ana kyautata zaton tattaunawar da za’a yi a taron zata bawa gwamnonin dake mulkin jihohin damar Æ™ara fahimtar abubuwan dake addabar a’lummar su tare da bijiro da hanyoyin gyara.
A baya bayan nan dai haren haren yan Boko Haram, ya tsananta a Borno da Yobe, wanda ko a Talata data gabata sai da suka kashe mutane 26 a Borno.
Jihohin arewa maso gabas sun haÉ—ar da States Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da Yobe.