Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya amince a riƙa biyan ma’aikatan jihar Naira dubu 75 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Gwamna Monday Okpebholo, ne ya sanar da hakan da bakin sa yayin bikin ranar ma’aikatan daya gudana a filin wasa na Ogbemudia, dake Benin, a yau Alhamis.
Tunda farko dai kungiyar ƙwadago ta NLC tace Naira 70,000 ta yi kaɗan a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya.
Gwamnan, yace anyi ƙarin albashin don ƙarfafa gwuiwar ma’aikata da kuma yaba musu.
Ya kuma roki ma’aikatan jihar dasu zamo masu sadaukarwa don inganta harkokin aikin gwamnati da Edo, baki ɗaya.