Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangogin su ta ƙasa ICPC ta bankaɗo cewa an karkatar da Naira biliyan 71.2, daga biliyan 100 da aka ware don bayar da tallafin bashin karatu da gwamnatin tarayya ta bijiro da shi.
ICPC tace zuwa yanzu ta gayyato wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa domin yin cikakken bayani akan yadda aka yi wadancan kudade suka zurare.


Mai magana da yawun ICPC Demola Bakare, ya bayyanawa manema labarai a birnin tarayya Abuja, cewa kwamitin hukumar na musamman yayi gaggawar ɗaukar mataki dangane da batun rashin kuɗin, karkashin jagorancin shirin bayar da tallafin bashin karatu wato NELFUND.
Manyan jami’an gwamnatin tarayya da ICPC ta gayyato akan batun kuɗin sun haɗar da daraktan ofishin kasafin kuɗi, babban akanta na tarayya, manyan jami’an babban bankin ƙasa CBN, da kuma daraktan shirin NELFUND.
Jawabin mai magana da yawun ICPC, yace binciken farko da aka gudanar ya bayyana cewa Naira biliyan 28.8 ne kaɗai yaje hannun waɗanda aka shirya bawa tallafin karatun, sannan ba’a san inda aka kai Naira biliyan 71.2 ba.