Shugaban ƙasa Tinubu zai kai ziyarar aiki jihar Katsina

0
21

Gwamnatin Katsina ta sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki jihar a ranar juma’a mai zuwa.

Bayanin hakan ya fito ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Bala Salisu Zango, yayin da yake zantawa da manema labarai.

Gwamnatin Katsina tace yayin ziyarar aikin ta kwana guda shugaban zai kaddamar da wasu manyan ayyukan cigaba da suka haɗar da aikin titin Eastern Bypass, wanda ya taso daga titin Dutsin-ma, zuwa hanyar Kano da Daura, sannan ya kare a yankin Yandaki, dake karamar hukumar Kaita.

Bayan wadancan ayyuka Tinubu, zai kuma kaddamar da wata katafariyar cibiyar sarrafa kayyakin gona a dai jihar ta Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here