Kwamandojin ƴan ta’adda sun miƙa wuya a Katsina

0
24

Daga jihar Katsina mai fama da matsalolin tsaro an samu wasu manyan jagororin ɓarayin daji da suka miƙa wuya tare da rungumar zaman lafiya, bayan yin sulhu da wata kungiya.

Ƙungiyar da ta shige gaba wajen yin sulhu da yan fashin dajin tace tuni wasu daga cikin mutanen suka ajiye makaman su, a daidai lokacin da wasu ke cigaba da riƙe makaman nasu don kariyar kai daga yan ta’addan da basu amince da yin sulhun ba.

Ɗaya daga cikin wadanda suka shige gaba wajen yin sulhun Kwamared Hamisu Sai’idu Batsari ya ce, daga cikin waɗanda suka miƙa wuya akwai Abu Radda da Maikada da Umar Blak da Tukur Dannajeriya.

Yace Abu Radda, shi kaɗai yana da mayaƙa da suka zarce 500.

Ya kuma ƙara da cewa, yan bindigan sun buƙaci gwamnati ta daina kama su ba tare da laifi ba, kuma idan sun yi laifi, a gurfanar da su a kotu kamar yadda doka ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here