Gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar ta bayar da lasisin kafa wasu kamfanoni biyar wanda ta ɗauke wa biyan kuɗin haraji na wani lokaci domin ƙarfafa musu gwuiwa.
Kamfanonin sun haɗa da na sarrafa ƙarafuna da wayoyin gine-gine, da wanda zai samar da makamashin lantarki da sayar da manyan injinan wutar lantarki.
Sannan akwai wani kamfani mai sarrafa sabulu da sauran kayan tsaftace jiki, da wanda zai sarrafa kayan gona, da mai samar da magunguna a kasar.
Wakiliyar BBC a Nijar Tchima Ila, ta ce waɗannan kamfanoni biyar za su samar da guraben aiki na dindindin kusan 3,000, da wasu dubbai na wucin gadi a shekaru biyar masu zuwa, musamman ga matasa.
Kamfanonin za su saka jarin da ya kai kusan cfa biliyan 250 a shekarun farko na soma aikin nasu.