Gwamnatin Kano zata kashe Naira biliyan 1.7 don magance matsalolin ƙarancin ruwan sha

0
24

Majalisar zartarwar Kano, ta amince a kashe Naira biliyan 1.7 wajen ingantawa da samar da ruwan sha a faɗin jihar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar yana mai cewa an amince da hakan yayin zaman majalisar zartarwa daya gudana a 28 ga watan Afrilu.

Kuɗaɗen sun haɗar da waɗanda ake siyo man dizel da Fetur a yankunan samar da ruwan sha a jihar Kano da kuma hukumar samar da ruwa ta jihar a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2025.

Zaman majalisar ya kuma jaddada kokarin da gwamnatin Kano keyi na garambawul a bangaren ruwa da samar da makamashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here