Gwamnatin Kano zata biya kansilolin Ganduje Naira biliyan 15.6

0
159
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf, ta amince a biya Naira biliyan 15.6, ga tsaffin kansilolin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, su fiye da 3000, dake ɗaukacin ƙananun hukumomin Kano 44.

Kuɗaɗen sun kasance na bashin da kansilolin ke bin gwamnatin, da suka ƙunshi alawus, da kuɗin barin aiki da sauran su.

Kansilolin da zasu amfana da kuɗin sune wadanda suka yi mulki a tsakanin shekarun 2014-2017, 2018-2020, sai na 2021 zuwa 2024.

Sanarwar da mai taimakawa gwamnan Kano a fannin yaɗa labarai Ibrahim Adam, ya fitar tace za’a biya kuɗaɗen a rukuni uku tsakanin watannin Afrilu, Mayu da Yuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here