Majalisar Shari’ar Musulunci ta ƙasa ta naɗa Dr. Bashir Aliyu Umar, a matsayin shugaban ta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Majalisar ta sanar da hakan a ranar Laraba, cikin wata sanarwar data fitar, inda sanarwar tace an naɗa Dr. Bashir Aliyu, a matsayin sakamakon shine mataimakin shugaban daya rasu.
A ranar Litinin data gabata ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81, wanda ya kasance a jihar Osun.
Sakataren Majalisar Nafiu Baba Ahmed, yace nan gaba kaɗan za’a sanar da mataimakin shugaban majalisar.
Sheikh Bashir, fitaccen malamin addinin Islama ne, kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke jihar Kano.