Tashin Bom ya kashe mutane da dama a jihar Borno

0
24

Rahotanni daga jihar Borno na cewa aƙalla mutum 26 ne suka rasu a ranar Litinin sakamakon tashin wani bom da motar da suke ciki ta taka a kan hanyar garin Rann zuwa Gmaboru Ngala.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa mutanen da abin ya rutsa da su sun haɗa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.

Bom ɗin da ake zaton ƙungiyar Boko Haram ce ta dasa binne shi, ya kuma jikkata aƙalla mutum da dama waɗanda suke asibiti domin samun kulawa.

Duk da cewa al’ummar yankin sun ɗora laifin kan ƙungiyar Boko Haram amma har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce uffan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here